Zambia na fargaba kan kwararowar 'yan gudun hijira
Kasar Zambia ta fara nuna fargaba kan dubban ‘yan gudun hijirar da ke ci gaba da kwararowa kasar sakamakon rikice-rikicen da su ke ci gaba da faruwa a kasashensu. Wata sanarwa Fadar shugaban kasar na Zambia Edgar Lungu ta fitar ta sanar da cewa ko cikin watan nan kimanin 'yan gudun hijira dubu 6 ne suka tsallako kasar daga makwabta.
Wallafawa ranar:
Galibin 'yan gudun hijirar a cewar sanarwar wadanda rikici ke i gaba da korowa ne daga Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo, lamarin da ke tilasta musu neman mafaka a kasashen makwabta.
Dubban mutane ne dai suka rasa rayukansu a rikicin kasar na Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo, yayinda wasu fiye da miliyan daya suka rasa muhalli. A yankin Kasai na jamhuriyyar Democradiya ta Congo.
Yanzu haka dai akwai ‘yan gudun hijira kusan dubu 60 a kasar ta Zambia, yawancinsu daga kasashen Angola da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo da Rwanda da kasashen Burundi da Somalia da kuma Uganda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu