Isa ga babban shafi
Mali-Sahel

Ziyarar Kwamitin tsaro a yankin Sahel

Tawagar masu ziyarar kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya karkashin jagorancin Jakadan Faransa a Majalisar Francois Delattre ya bayyana matukar damuwa ga kungiyoyin da suka rattaba hannu a yarjejeniyar cimma zaman lafiya a kasar Mali.

Shugaban kasar Faransa da wasu Shugabanin kasashen Sahel a Mali
Shugaban kasar Faransa da wasu Shugabanin kasashen Sahel a Mali REUTERS/Luc Gnago
Talla

An dai fara ziyarar ne daga ranar 19 zuwa 23 ga wannan wata na Oktoba, inda ake saran tawagar za ta ziyarci dukkanin kasashen yankin Sahel biyar da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar.

François Delattre ya ce babban kalubalen da rundunar hadakar ke fuskanta a yanzu bai wuce batun kudaden tafiyarwa ba, yana mai cewa yayin wannan ziyara za su kara fahimtar da kasashen duniya dangane da muhimmancin kafa rundunar don yaki da ta'addanci.

kasashen na G5-Sahel da suka kunshi Burkinafaso da Chadi da Mali da Mauritania da kuma Jamhuriyyar Nijar, tuni suka samar da kimanin dakaru dubu don kafa wata babbar rundunar da za ta yi yaki da ayyukan ta’addanci da suka kunshi fataucin miyagun kwayoyi da makamai a wannan yanki na Sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.