Kungiyar G5 Sahel za ta samu taimakon MDD
Tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ta ziyarci yankin Sahel, ta ce ko shakka babu kasashen duniya za su taimakawa yankin domin kaddamar da rundunar G5-Sahel wadda za ta yaki ayyukan ta’addanci.
Wallafawa ranar:
Jakadun Majalisar Dinkin Duniya sun kammala wannan ziyarar ne a Burkina Faso, a kokarin ganin an kafa rundunar wanzar da tsaro da kuma fada da ayyukan ta’addanci yankin wanda ya kunshi kasashe biyar.
Jakadan Faransa a Majalisar Dinkin Duniya wanda ke cikin wannan tawaga Francois Delattre, ya bayyana wa manema labarai a birnin Ouagadougou na Burkina Faso cewa, wannan rangadi ya ba su damar ganawa da shugabannin kasashen yankin dangane da sanin muhimmancin gaggauta kafa wannan runduna.
Kasashen Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritaniya da kuma Nijar sun yanke shawarar kafa rundunar mai suna G5-Sahel ne domin tabbatar da tsaro a yankunan iyakokinsu da yanzu haka ke fama da ayyukan ta’addanci.
Rundunar za ta kunshi dakaru dubu biyar, sai dai ana bukatar kudi yuro milyan 224 domin daukar dawainiyarta, kudaden da har yanzu bayanai ke cewa an gagara samar da su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu