Isa ga babban shafi
Najeriya

Mahara sun kashe mutane 13 a Maiduguri

Wasu mata ‘yan kunar bakin wake su uku sun tarwatsa kansu tare da kashe mutane 13 sannan suka raunata wasu 16 a birnin Maiduguri da ke Najeriya.

Wani harin 'yan Boko Haram a garin Maiduguri a 2009
Wani harin 'yan Boko Haram a garin Maiduguri a 2009 (Photo : Reuters)
Talla

Bayanai sun tabbatar da cewa da farko wata ‘yar kunar bakin wake ce ta tarwatsa kanta da misalin karfe 9 na daren lahadi a harabar wani gidan cin abinci, kafin daga bisani wasu ‘yan mata biyu su tayar da nasu bama-baman.

Duk da cewa ba wata kungiya da ta fito domin daukar nauyin kai hare-haren na daren jiya, to sai dai ana danganta lamarin da kungiyar Boko Haram da ta share tsawon shekaru tana aikata ayyukan ta’addanci a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau
Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau News Ghana

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.