Isa ga babban shafi
Togo

Jam'iyyun adawar Togo zasu yi tarzomar kwanaki Uku a jere

Jam’iyyun adawa a Togo sun bukaci magoya bayansu da su fito domin gudanar da tarzoma a tsawon kwanaki uku jere a juna a cikin watan nuwamba mai zuwa.

Magudun 'yan adawa Jean-Pierre Fabre na Togo
Magudun 'yan adawa Jean-Pierre Fabre na Togo REUTERS/Stringer
Talla

Eric Dupuy, kakakin ‘yan adawa ya bayyana cewa za su yi zanga-zangar ne a ranakun 7 da 8 da kuma 9 ga watan gobe a birnin Lome domin tilasta wa Faure Gnasingbe daga karagar mulki.

Ita ma kasar Gambia ta bukaci kungiyar kasashen Afirka ta AU da kungiyar kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS da su lallabi shugaba Gnassingbe ya sauka daga mukamin sa domin kawo karshen tashin hankalin da ake samu.

Ministan harkokin wajen Gambia Ousainou Darboe ya bayyana haka a tattaunawar da suka yi da kamfanin dillancin labaran Reuters.

Kalaman ministan na nuna yadda wasu kasashen Afirka ta Yamma suka fara dawowa daga rakiyar shugaba Gnassingbe wanda ya gaji mahaifin sa a shekarar 2005, bayan ya kwashe 38 a karagar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.