Tubabben mataimakin shugaban Zimbabwe ya koma gida
Tubabben mataimakin shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya koma kasar, mako daya bayan da shugaba Robert Mugabe ya sanar da cewa ya tube daga matsayin, lamarin da shi ne dalilin kutsen soji a fagen siyasar kasar.
Wallafawa ranar:
Wani na hannun daman Emmerson ya tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, jagoran nasu ya koma gida a daidai wannan lokaci da kungiyar kasashen Kudancin Afrika SADC ke kokarin samar da sulhu tsakanin Mugabe da kuma sojojin da ke ci gaba da yi ma sa daurin talala a gidansa.
Bayanai sun tabbatar da cewa Robert Mugabe ya bayyana cewa ba zai sauka daga mukaminsa ba kamar dai yadda sojojin ke bukata, yayin da wasu majiyoyi ke cewa Mugabe na adawa ne da duk wani mataki da zai bai wa Emmerson damar ya gaje shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu