Shugabanin kasashen Afrika sun bukaci magance rikicin Togo
Shugabannin Kasashen Afirka sun bukaci shata hanyar magance rikicin siyasar kasar Togo domin kaucewa barkewar tashin hankali a fadin kasar.
Wallafawa ranar:
Shugabannin kasashen Najeriya da Cote d’Ivoire da Ghana da Burkinan Faso da Benin da kuma Guinea sun bukaci tattaunawa tsakanin wakilan Gwamnatin Togo da kuma Yan adawa ba tare da gindaya sharudodi ba.
Yan adawar Togo sun kwashe dogon lokaci suna gudanar da zanga zanga domin kawo karshen mulki shugaba Faure Gnassingbe wanda shi da mahaifin sa suka kwashe kusan shekaru 50 suna mulkin kasar.
Shugabannin na Afirka sun bayyana fargabar cewar rashin warware matsalar na iya haifar da rikicin da zai shafi Afirka ta Yamma baki daya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu