Isa ga babban shafi

Benin: Kotu ta soke dokar haramtawa ma'aikata shiga yajin aiki

Kotun kolin Jamhuriyar Benin ta soke dokar da gwamnatin kasar ta kafa, wadda ta haramtawa ma’aikatan kasar shiga yajin aiki.

Shugaban Jamhuriyar Benin Patrice Talon
Shugaban Jamhuriyar Benin Patrice Talon REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Hukuncin kotun ya zo ne bayan shafe kwanaki uku da aka yi, dubban ‘yan kasar suna gudanar da zanga-zangar adawa da dokar.

A watan Disambar da ya gabata ne majalisar dokokin Jamhuriyar Benin ta mince da kudurin dokar da shugaban kasar Patrice Talon ya gabatar mata na haramtawa Sojoji, ‘yan sanda, ma’aikatan lafiya da kuma ma’aikatan sashin shari’ar kasar shiga yajin aiki don tilastawa gwamnati biyan bukatunsu.

Shugaba Talon ya ce ya kafa dokar ce don kyautata tattalin arzikin Jamhuriyar ta Benin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.