Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta ce daliban Dapchi 110 ne har yanzu ba a ji duriyarsu ba

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewar, ya zuwa yanzu dalibai mata 110 ne daga makarantar sakandaren Dapchi da har yanzu ba’aji duriyar su ba bayan harin da kungiyar boko haram ta kai makon jiya.

Tawagar gwamnatin Najeriyar karkashin jagorancin ministan yada labaran kasar Alhaji Lai Muhammad, bayan kammala ganawa da iyayen daliban ta ce akwai akalla yara 110 da ba a ji duriyarsu ba tun bayan harin na ranar litinin.
Tawagar gwamnatin Najeriyar karkashin jagorancin ministan yada labaran kasar Alhaji Lai Muhammad, bayan kammala ganawa da iyayen daliban ta ce akwai akalla yara 110 da ba a ji duriyarsu ba tun bayan harin na ranar litinin. REUTERS/Ola Lanre
Talla

Ministan yada labarai Lai Mohammed, wanda ya sake jagorantar tawagar gwamnatin tarayya zuwa Yobe a karo na hudu tun bayan bacewar 'yan matan a litinin din makon da ya gabata,ya sanar da hakan bayan wani taro da suka yi da Gwamnan Jihar tare da kwamishinonin sa da kuma shugabannin makarantar Sakandiren ta Dapchi.

Ministan wanda ya ce tuni aka baza sojoji da Yan Sanda domin nemo Yam matan, ya kuma ce an umurci Yan Sanda da jami’an Civil Defence da su ci gaba da aikin bayar da tsaro a ilahirin makarantun da ke Jihar.

Ziyarar tawagar gwamnatin tarayyar na zuwa ne a dai dai lokacin da Gwamnan jihar Ibrahim Geidam ke ci gaba da zargin Rundunar sojin Najeriyar da sakaci bayan janye jami'anta, matakin da ya ce shi ya taka muhimmiyar rawa wajen bayar da dama ga mayakan na Boko Haram su sace yaran.

Tun a ranar Litinin din da ta gabata ne wasu mayaka da ake zargin 'yan boko haram ne sanye da kayan soji suka kai sumamen makarantar sakandiren 'yan matan da ke garin Dapchi tare da yin awon gaba da adadi mai yawa na daliban.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.