Isa ga babban shafi
Masar

Kristocin Masar sun ce al-Sisi ne dan takararsu

Yayin da lokacin gudanar da zaben shugaban kasar Masar ke karatowa, kibdawan kasar sun bayyana aniyarsu ta goyan bayan shugaba Abdel Fatah al Sisi saboda irin goyan bayan da ya ke bai wa jama’arsu a kasar.

Abdel Fattah al-Sisi, shugaban  Masar
Abdel Fattah al-Sisi, shugaban Masar REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Yanzu haka a unguwannin Kibdawan, an saka hotunan shugaba al Sisi tare da Fafaroma Tawadros na II, jagoransu na addini, wanda ke nuna irin goyan bayan da suke yi wa shugaban.

Edward Tawfik, wani dattijo mai shekaru 60 daga cikin Kibdawan, ya ce babu wani dan takara da ya kai al Sisi a gare su.

Ana sa-ran gudanar da zaben ne ranakun 26 zuwa 28 ga wannan wata na masi, kuma ba wani fitataccen dan siyasa a cikin mutanen da ke shirin karawa da shugaban wanda ya kwaci mulki da karfi daga hannun Mohammad Morsi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.