Isa ga babban shafi
Najeriya

Kalaman Buhari kan Matasa na ci gaba da shan suka a Najeriya

Kalaman shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na cewa matasan kasar malalata ne kuma marasa ilimi da ba sa tashi tsaye don neman na kansu face mafarkin samun kowacce kulawa kyauta daga gwamnati, na ci gaba da shan suka daga bangarorin siyasa da kuma na matasan.

Tuni dai kalaman shugaban suka fara fuskantar mummunar suka daga matasan Najeriyar ko da ya ke dai wasu na ganin akwai kanshin gaskiya a kalaman na Muhammadu Buhari.
Tuni dai kalaman shugaban suka fara fuskantar mummunar suka daga matasan Najeriyar ko da ya ke dai wasu na ganin akwai kanshin gaskiya a kalaman na Muhammadu Buhari. TheCable
Talla

Muhammadu Buhari yayin wani jawabinsa a taron kasashe renon Ingila da ke ci gaba da gudana a birnin London, ya ce kimanin kaso 60 na al’ummar kasar da galibinsu matasa ne, kashi 30 basu je makaranta ba, yayinda suke zaune kara zube bisa tunkahon kasarsu na da arzikin man fetur.

A cewar Muhammadu Buhari makamantan matasan yayin da suke jiran a yi musu hidimar karatu, lafiya dama samar musu da muhalli kyauta ba tare da jibinsu ba.

Tuni dai kalaman na Muhammadu Buhari ya fuskanci mummunar suka suka daga matasan wadanda suka ce shugaban bai musu adalci ba, ko da yake dai wasu na ganin akwai kanshin gaskiyar a batun na Muhammadu Buhari.

A bangare guda shima tsohon mamba a jam'iyyar APC mai mulkin kasar kuma tsohon shugaban Najeriyar Atiku Abubakar ya ce bai kamata Buharin ya alakanta matasan Najeriyar da malalata ba.

Kalaman Shugaban dai na iya zama gagarumar matsala ga bukatarshi ta sake tsayawa takarar shugabancin Najeriyar a 2019 musamman ganin yadda a baya ya ke da miliyoyin matasa magoya baya, kuma kalaman ka iya tunzura su wajen kin zabenshi a 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.