Isa ga babban shafi

Dubban 'yan adawa suna zanga-zanga a Madagascar

‘Yan adawa sama da dubu a kasar Madagascar sun ci gaba da gudanar da zanga-zanga a babban birnin kasar Antana-narivo kwanaki takwas a jere, inda suke neman tilastawa shugaban kasar, Hery Rajao-narimam-Pianina yayi murabus.

Dubban 'yan adawa a kasar Madagascar, yayin zanga-zangar neman shugaban kasa a yayi murabsu a babban birnin kasar, Antananarivo.
Dubban 'yan adawa a kasar Madagascar, yayin zanga-zangar neman shugaban kasa a yayi murabsu a babban birnin kasar, Antananarivo. RIJASOLO / AFP
Talla

Zanga-zangar na zuwa ne, yayin da ya rage watanni bakwai a gudanar da zaben shugaban kasar da ‘yan majalisu, wanda ‘yan adawa ke zargin za’a tafka magudi a cikinsa.

Zalika ‘yan adawar suna zargin gwamnatin Rajao-Narimam-Pianina da yunkurin hana wasu manya adawa tsayawa takarar shugabacin kasar, ta hanyar kafa wasu sabbin dokokin zabe.

Zuwa yanzu mutane 2 suka mutu a zanga-zangaar, yayinda wasu 16 suka jikkata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.