Isa ga babban shafi
Madagascar

Wadanda annoba ke shafa a Madagascar na karuwa

Ma’aikatar lafiya ta kasar Madagascar ta ce zuwa yanzu sama da mutane 74 ne suka rasa rayukansu cikin watanni biyu, sakamakon kamuwa da cutar zazzabi mai zafi.

Wasu jami'an lafiya na kasar Madagascar yayin da suke kan aikin fesa maganin kashe kwari da tsaftace muhalli a Kasuwar Anosibe dake yankin Antananarivo a ranar 10, Oktoba,2017.
Wasu jami'an lafiya na kasar Madagascar yayin da suke kan aikin fesa maganin kashe kwari da tsaftace muhalli a Kasuwar Anosibe dake yankin Antananarivo a ranar 10, Oktoba,2017. PHOTO: AFP
Talla

Cikin rahoton da ma’aikatar lafiyar ta fitar, ta ce daga watan Agustan daya gabata zuwa yanzu, akalla mutane 804 ta samu rahoton sun kamu da cutar, wadda ta samo asali daga beraye, yayinda kuma kwari ke bazata.

Tun daga shekarar 1980, kasar Madagascar ke fuskantar annobar barkewar cutuka a duk shekara, mafi akasarin lokuta a tsakanin watannin Satumba da Afrilu.

Hakan kuwa na da nasaba da yadda beraye da dangoginsu ke tserewa daga dazuka zuwa cikin jama’a don gujewa gobarar dajin da akan samu a lokutan.

Sai dai hukumar lafiya da Duniya WHO ta ce a wannan karon annobar cutar na da banbanci da sauran da aka fuskanta a baya, ganin cewa ta bazu zuwa cikin birane a maimakon kauyuka da ta fi shafa a baya.

Daga cikin manyan alamun kamuwa da cutar akwai zazzabi mai zafi da kuma tari.

Tuni dai hukumar ta WHO ta aike da maganin cutar akalla miliyan 1 da dubu 200 zuwa kasar don shawo kan annobar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.