Harin kunar bakin wake ya hallaka masallata a Mubi
Mutane da dama ake kyautata zaton sun mutu a wani harin kunar bakinn wake da ake zargin Boko Haram da kaddamarwa a wani masallaci da ke garin Mubin jihar Adamawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Wallafawa ranar:
Lamarin ya faru ne a anguwar Wuro-Burode lokacin da al’umma ke tsaka da sallar Azahar.
Ko da ya ke dai har yanzu ba a kai ga tantance adadin mutanen da suka mutu ba, amma rahotanni sun adadin na da yawa ba ya ga wadanda suka jikkata.
Wasu shaidun gani da ido sun sanar da cewa wani karamin yaro ne daure da bom jikinsa ya shiga cikin masallacin tare da tayar da bom din.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu