Isa ga babban shafi
Kamaru

An kashe 34 daga cikin yan awaren Kamaru

Rahotanni daga kasar Kamaru na cewar akalla yan aware 34 aka kashe a garin Menka dake Yankin da ake amfani da Turancin Ingilishi.

Talla

Wannan shine tashin hankali mafi muni da aka samu a yankin tun bayan barkewar tashe-tashen hankulan da ke da nasaba da neman yanci.

Agbor Balla Nkongho, wani lauya mai kare hakkin Bil Adama a Yankin ya ce an samu gawawaki 34 yammacin juma’a, ba tare da sanin wanda ya kashesu ba.

Wata majiya ta daban ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewar ta ga gawawaki 29, cikin su harda wadanda aka lalata da harbin bindiga a wajen kusa da wata makaranta.

Kakakin sojin kasar Kanar Didier Badjeck ya shaida wa manema labarai cewar jami’an tsaro sun yi arangama da wasu mutane da suka taru a wani otel a Menka da ake zargin yan aware.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.