Faransa za ta kasance mai shiga tsakani a rikicin Libya
A ranar talata mai kamawa ne Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai ganawa da wasu magabatan Libya a Paris na kasar Faransa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Taron zai hada Firaministan kasar Fayez Al Sarraj, Janar Khalifa Haftar, Shugaban majalisar wakilan kasar Aguila Salah Issa da Shugaban kwamity zartarwa Khaled Al Mishri.
A wannan ganawa Shugaban Faransa na fatan samun hadin kan Shugabanin domin kawo karshen tankiyar da ake fuskanta tareda taimakawa don samar da gwamnati a kasar da zata samu goyan baya daga kasashen Duniya.
Shugaban Faransa ya gayato kasashen dake da hannu a rikicin Libya da sauren Shugabanin kasashe aminan Libya da za su iya taka gaggarumar rawa a zaman taron na Paris don kawo karshen rikicin kasar ga baki daya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu