Isa ga babban shafi
Kenya

Gwamnatin Kenya za ta kawo karshen rashawa a kasar

Babban mai bincike na gwmanatin Kenya ya ce rashawa na neman durkusar da ayyukan hukuma a kasar.

Masu zanga-zanga a kasar Kenya
Masu zanga-zanga a kasar Kenya REUTERS/Baz Ratner
Talla

Edward Ouko wanda ke zantawa da manema labarai a birnin Nairobi, kan binciken da ake yi dangane da wawashe kudaden hukumar aikin bautawa kasar, ya ce akwai hadin baki tsakanin kananan ma’aikata da manyan jami’an gwamnati domin karkata dukiyar kasar.

Matakin gudanar da bincike a kan bankunan ya biyo bayan cafke wasu manyan jami’an hukumar bautawa kasar ne da aka cafke kan zargin su da hannu a wannan almundahna.

Rahotanni sun bayyana sunayen bankuna 9, da wata ƙungiyar hadin gwiwa ta kudi, a matsayin cibiyoyin da jamian yan sanda da kuma masu bincike a babban bankin kasar zasu bincika.

Masu bada rancen kudin sun hada da Babbar cibiyar samar da rancen kadarori ta kasar kenya, kampanin KCB, da kuma Ƙungiyar Amincin Ƙididdiga ta Kamfanin Kenya.

Darektan binciken laifuka, George Kinoti, ya shaidawa manema labarai cewa adadin wadanda aka zarga da aikata laifin dai-dai ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.