Isa ga babban shafi
MDD-lIBYA

Gwamnatin hadaka a Libya na neman agajin Majalisar Dinkin Duniya

Gwamnatin hadin kan kasar Libya a yau Talata ta bukaci kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kawo karshen fitar da haramtaccen man fetur din da bata gari ke yi daga kasar ba bisa ka’ida ba.Libyan wadda ta yi fama da tashe tashen hankula tun bayan da tsagin gwamnati da ke hamanya ta yi nasarar karbe ikon tashar jiragen mai.

Shugaba Khalifa Haftar na Libya tare da Firaministan kasar da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya Fayez al-Sarraj.
Shugaba Khalifa Haftar na Libya tare da Firaministan kasar da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya Fayez al-Sarraj. Fethi Belaid, Khalil Mazraawi/AFP
Talla

Bukatar gwamnatin Libyan na zuwa ne bayan kwace ikon da Halifa Khaftar ya yi da wasu tashoshin jiragen mai biyu a yankin gabashin kasar wadanda ya ce zai mika su ga shugabancin yankin gabashin da ba a kai ga tantancewa ba.

A cewar gwamnatin hadin kan ta Libya da ke birnin Tripoli matakin na Halifa Haftar zai haifar da sake rarrabuwar kawunan shugabanni a kasar.

Tun a jiya litinin ne dakarun Khalifa Haftar suka kwace iko da bangaren man fetur a kasar ta libiya bayan wani mumunar fafatawa jina-jina na tsawon kwanaki 10 tsakanin bangarorin biyu

Gwamnatin hadin kan kasar ta kara da cewa mika kudaden man fetur din ga kwamnatin da ba’a san da ita ba wanda Haftar ke goyon baya zai iya sanyaya gwiwar dukkan kokarin da kasashe duniya har ma da kasar ke yi a wa’annan shekaru na ganin an maido da kwanciyar hankali a kasar.

Kasar Libya dai ta yi ta fama da tashe tashen hankula tun shekarar 2011 da soji suka yi nasarar kashe dadadden shugaban kasar, Mu’ammar Gaddafi tare da barin yan hamayyan biyu masu rike da iko a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.