Wani hari ya halaka dakarun Haftar a Libya
Wasu tagwayen bama-bamai da aka tayar a garin Derna na kasar Libya, sun yi sanadiyyar mutuwar da kuma raunana wani adadi na dakarun Janar Khalifa Haftar da ke rike da muhimman yankunan gabashin kasar.
Wallafawa ranar:
Wani jami’i a yankin mai suna Khalifa al-Abidi, ya ce ga alama magoya bayan kungiyar IS ne suka kai harin a dai dai lokacin da mayakan na Haftar ke kokarin kakkabe su daga garin na Derna.
Janar Khalifa Haftar, hafsan sojin da ke rike da muhimman yankuna a kasar Libya, kafin cirawar sa zuwa Faransa domin neman magani ya umurci dakarunsa da su hana wa jiragen ruwan kasashen ketare matsowa kusa da gabar ruwan kasar.
Tun bayan kisa da kuma kawar da marigayi Muammar Ghadafi daga madafan ikon Libya, kasar ta fada cikin rikici.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu