Isa ga babban shafi
Gabon-Tattalin arziki

Ali Bongo na Gabon ya dau matakin tsuke bakin aljihu

Shugaban kasar Gabon Ali Bongo ya kori kashi 40 cikin dari na jami’an dake aiki a fadar sa, a wani yunkuri na rage facaka da kudin gwamnati, inda ya kira Ministocinsa da suyi koyi da shi.Tuni dai matakin ya haifarar da cece-kuce dama fargaba tsakanin jami’an da ke ayyuka karkashin ministocin kasar. 

Ali Bongo ya umurci daukacin ministocin kasar da su kasance da wakilai 16 kachal a maimakon sama da 40 da suke da su tun farko.
Ali Bongo ya umurci daukacin ministocin kasar da su kasance da wakilai 16 kachal a maimakon sama da 40 da suke da su tun farko. REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Wata sanarwa daga majalisar ministoci ta fito da jerin sunayen wasu takaitattun mutane da suka rage a matsayin abokan aikin shugaban kasa, yayinda wadanda ba suga sunayen su ba kuwa zasu koma ma’aikatunsu ta asali.

Rahotanni sun ce shugaban Ali Bongo zai yi aiki ne kadai da kusoshin gwamnatin da suka zame masa wajibi kamar daraktan fadar sa da kuma sakataran gwamnatin kasar.

Bayan misali da ya nuna da kansa, Ali Bongo ya umurci daukacin ministocin kasar da su kasance da wakilai 16 kachal a maimakon sama da 40 da suke da su tun farko.

Kazalika gwamnatin ta Gabon ta haramtawa duk wani jami’inta tafiye-tafiye a kujerun katsaita yayin duk wata tafiya da za su yi da ta shafi lalitar gwamnati yayinda aka haramta musu amfani da motocin da kudinsu ya haura Euro dubu 45.

Yayin wani taro manema labarai, kungiyar kwadagon kasar ta yi na'am da matakin tsuke bakin aljihun na gwamnati sai da ta yi kakkausar suka game da kudirin gwamnati na dakatar da daukar ma’aikata har nan da shekaru uku masu zuwa.

Haka zalika kungiyar ta kwadago ta ki amincewa da batun rage albashin ma'aikata a fadin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.