Isa ga babban shafi
Najeriya

Ma'aikatun Najeriya 308 sun kashe biliyan149 ba bisa ka'ida ba - rahoto

Wani rahoto kan yadda kasafin kudin Najeriya na 2016 ya gudana daga ofishin babban mai binciken kudi na kasar Mr Anthony Ayine ya nuna yadda wasu ma’aikatu da sassan gwamnati 308 suka kasha kudaden da suka wuce kima da yawansu ya kai Naira biliyan 149 da miliyan biyar.

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Bukola Saraki, tare da takwaransa na Majalisar wakilai Yakubu Dogara.
Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Bukola Saraki, tare da takwaransa na Majalisar wakilai Yakubu Dogara. NigerianEye
Talla

Rahoton dauke da sa hannun Mr Ayine ya ce matakin kashe kudaden fiye da kima da ma’aikatun gwamnatin Najeriyar 308 suka yi a shekarar 2016 alamu ne na gazawa musamman bayan rashin gabatar da hujjoji kan yadda aka kasha kudaden

Rahoton ya nuna cewa ma’aikatun da suka kashe kudaden fiye da kima a 2016 sun kunshi cibiyar bunkasa mata ta Najeriyar wadda ta kashe Naira biliyan 3 da miliyan 82, akwai kuma hukumar agajin gaggawa da itama ta kashe kusan biliyan 11.

Sauran sun kunshi hukumar ‘yan sanda da ta kashe miliyan 284, tare kuma da asusun tallafawa manyan makarantu da shi kuma ya kashe Naira biliyan guda da miliyan 12, dukkaninsu bayan kasafin da aka ware musu a shekarar ta 2016.

A bangare guda kuma rahoton ya nuna yadda aka rarraba wasu tsabar kudade da yawansu ya kai Naira Biliyan 12 zuwa wasu Ofisoshin gwamnatin Tarayyar wadanda ba a fayyace abin da aka yi da su ba.

Tuni Ofishin mai binciken kudin ya mika wannan rahoto ga majalisun kasar don bibiyarsa tare da nazartar matakan da za a dauka a nan gaba.

Rahotanni sun ce tun a watan Yunin da ya gabata rahoton ya isa gaban Majalisun Najeriyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.