Isa ga babban shafi
Kamaru

An karbo yara 'yan makaranta 79 da aka yi garkuwa dasu a Kamaru

Daukacin yara ‘yan makaranta 79 da aka sace a yankin nan dake amfani da turancin Inglishi mai fama da rikicin yan aware dake arewa maso yammacin kasar Kamaru a ranar litanin da ta gabata, sun samu sallama a yau laraba, kamar yadda ministan sadarwar kasar haka kuma kakakin gwamnati,  Issa Tchiroma Bakari ya sanar da kamfanin dillancin labaran AFP.

ministan sadarwar kasar Kamaru Issa Tchiroma Bakary na fira da yan jarida a  Octoba 2014.
ministan sadarwar kasar Kamaru Issa Tchiroma Bakary na fira da yan jarida a Octoba 2014. AFP/Pacome Pabandji
Talla

Issa Tchiroma Bakari ya ce, dukkanin dadiban 79 an sallamo su, sai dai bai bayyana cikin irin yanayin da aka sako yaran a ciki ba.

Yaran  dai dalibai ne a makarantar Presbyterian Secondary School dake Bamenda  babban birnin yankin arewa maso yammacin kasar Kamaru , an kuma sace su ne tare da wasu malamansu guda 3

Sai dai ministan Bakary yace a halin yanzu ba ya da wata masaniya dangane da halin da malaman uku ke ciki

Za a iya cewa dai, a karo na farko ke nan a kasar Kamaru aka samu faruwar irin wannan garkuwa ta gungun  jama’a, salon da kungiyar Boko Haram dake yaki  arewacin kamaru da tarayyar Najeriya mai makwabtaka da kasar ke amfani da shi, inda a shekara ta 2014 kungiyar ta yi garkuwa da yara 'yan matan sakadaren Chibok su 200, al’amarin da ya haifar da bacin rai da tofin Allah tsine a kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.