'Yan bindiga sun sace dalibai 79 a yankin 'yan aware na kasar Kamaru
Rahotanni daga kasar Kamaru sun ce wasu Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu daliban makarantu 79 a yankin da ake fama da rikicin 'yan awaren dake fafutukar samun yanci.
Wallafawa ranar:
Wata majiyar gwamnatin kasar ta ce an sace daliban ne tare da malamin su da kuma shugaban makarantar hadi da direban su.
Su dai wadannan dalibai suna karatu ne a makarantar Sakandaren Presbyterian da ke Bamenda, daya daga cikin Yankuna ada kae samun hare hare.
Wani faifan bidiyo da 'Yan waren suka saki a Internate jim kadan bayan sace daliban sun nuno yaran na fadin sunayensu tare da rokon a ceto su, sai dai bayanan 'yan tawayen na nuni da cewa ba za a saki daliban har sai an amince musu da kafa kasar Ambazonia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu