Amurka-Chadi
Amurka ta bai wa Chadi motoci da kwale-kwale don yakar ta'addanci
Kasar Amurka ta bai wa Chadi motocin soji da kwale kwale da kudin su ya kai kusan Dala miliyan guda da rabi domin yaki da Yan ta’adda.
Wallafawa ranar:
Talla
Samantah Hero, mai Magana da yawun rundunar sojin Amurka da ke aiki a Afirka, ta ce barazanar kungiyar boko haram da IS na zuwa ne ta ruwa da kuma kasa daga tafkin Chadi da Arewa maso Gabashin Najeriya.
Jakadan Amurka a Chadi, Richard K. Bell ya ce taimakon ya hada da motoci 6 da kwale kwale 6, yayin da sojojin Chadi 13 yanzu haka su ke samun horo a Amurka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu