Isa ga babban shafi
Najeriya-Amurka

Lauyan Trump ya zargi musulmin Najeriya da kisan Kirista dubu 60

Wani Faifan bidiyo da lauyoyin shugaban Amurka Donald Trump suka sanya shafin dandalin sada zumuntar facebook ya ce makiyaya Musulmi sun kashe kiristoci 60,000 a tsakiyar Najeria.

Taswirar Najeriya.
Taswirar Najeriya. CIA
Talla

Binciken da kamfanin dillancin labaran Faransa ya gudanar kan zargin da lauyan shugaba Donald Trump Jay Sekulow yayi a bidiyon da aka wallafa a facebook ranar 23 ga watan Nuwamba, cewar kabilar Fulani Musulmi ta kashe kiristoci manoma 60,000, ya gano cewar ba haka lamarin yake ba.

Shidai faifan bidiyon ya samo assail ne daga wata Cibiyar tabbatar da shari’a da ake kira ‘American Centre for Law and Justice’ ta kiristoci dake Washington.

Binciken na kamfanin dillancin labaran Faransa domin tabbatar da gaskiyar labarin, ya gano cewar bah aka labarin yake ba, saboda babu wata shaida ta hakika dake tabbatar da haka, duk da yake an samu tahse tashen hankula daban daban.

Kamfanin dillancin labaran yace wani adadin mamata da aka dangata da wani addini, kuma kokarin tattara alkaluman mamata a rikice rikicen da aka samu ya bada adadin da bai kai 60,000.

Kamfanin dillancin labaran yace yan ra’ayin rikau a Amurka na amfani da wannan rahoto domin cimma manufar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.