Isa ga babban shafi
DR Congo

Congo ta katse intanet saboda zaben kasar

Manyan kasashen yammacin duniya sun bukaci Jamhuriyar Demokradiyar Congo da ta maido da hanyar sadarwar Intanet bayan katse ta kwana guda da gudanar da zaben shugabancin kasar.

Ana ci gaba da kidayar kuri'un da aka kada a zaben Jamhuriyar Demokradiyar Congo
Ana ci gaba da kidayar kuri'un da aka kada a zaben Jamhuriyar Demokradiyar Congo REUTERS/Baz Ratner
Talla

Kasashen da suka yi wannan kiran sun hada da Birtaniya da Faransa da Netherlands da Belgium da Sweden da Amurka da Canada da Switzerland.

Kasahen sun kuma goyi bayan bukatar manyan kungiyoyin da ke neman a ba su izinin shiga cibiyoyin da ake kidayar kuri’un da aka kada a ranar Lahadi.

Mahukuntan Jamhuriyar Congo sun kuma katse hanyar tura sakwanni ta wayoyin hannu kamar yadda kamfanin Vodacom ya tabbatar.

Kazalika tashar Radio France International ta ce, tun a yammacin ranar Litinin aka haifar da tarnaki kan hanyoyin watsa shirye-shiryenta a Congon.

tashar ta yi aiki tukuru wajen daukan labaran zaben kasar.

A halin yanzu dai, ana ci gaba da kidayar kiri’u kafin fitar da sakamakon da zai bayyana wanda zai gaci shugaba Joseph Kabila wanda ya shafe shekaru 18 akan karagar mulki.

Ana saran fitar da sakamakon karshe a ranar Lahadi mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.