Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

Amurka ta aike da sojojinta zuwa Gabon kan zaben Congo

Manyan kasashen Nahiyoyin Afrika da Turai na ci gaba da matsawa gwamnatin Joseph Kabila na Jamhuriyar Congo, kan tilas ta mutunta ra’ayin ‘yan kasar da suka kada kuri’a a zaben da ya gudana rana 30 ga watan Disamba, 2018.

Wasu jami'an hukumar zaben Jamhuriyar Congo, yayin kidayar kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasar.
Wasu jami'an hukumar zaben Jamhuriyar Congo, yayin kidayar kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasar. AFP / Caroline Thirion
Talla

Gargadin daga ciki da wajen Nahiyar Afrika na zuwa a dai dai lokacin da al’ummar Jamhuriyar ta Congo ke dakon sakamakon zaben shugabancin kasar cikin zulumi.

Yayin da kungiyar Tarayyar Afrika AU, da kungiyar Tarayyar Turai suka bukaci gwamnatin Kabila ta kaucewa yunkurin sauya sakamakon zaben, ita kuwa Amurka, gargadi ta yi kan cewa za ta kakaba takunkumi kan duk wanda ya taka rawa wajen murde sakamakon zaben.

Tuni dai Amurka ta aike da sojojinta zuwa Gabon da ke makwabtaka da Jamhuriyar Congo.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce dakarun kasar 80 ne suka samu isa Gabon tun a ranar Laraba, domin baiwa Amurkawa da kuma kadarorin kasar da ke Jamhuriyar ta Congo kariya, idan har rikici ya barke a babban birnin kasar Kinshasa.

A ranar 30 ga watan Disamban da ya gabata, al’ummar Jamuriyar Congo suka kada kuri’unsu a zaben shugabancin kasar, wanda aka fafata tsakanin ‘yan takara 21 ciki har da Emmanuel Ramazani dan takarar shugaba mai ci Joseph Kabila.

Sai dai zulumin da al’umma ke ciki ya karu ne, bayan da shugaban hukumar zaben kasar ta CENI, Corneille Nangaa, ya sanar da yiwuwar dage ranar sanar da sakamakon zaben daga ranar Lahadi 6 gawa watan Janairu, saboda jinkirin da suke fuskanta wajen tattara sakamakon zaben a wasu sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.