Congo:Gwamnati ta yi wa shugabannin Kataloki kashedi
Kawancen jam’iyyun da ke mara wa gwamnati baya a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, sun zargi shugabannin mujami’ar katolika da yin shisshigi a cikin lamurran siyasa, bayan da majalisar koli ta Katolikan ta yi ikirarin cewa ta san wanda ya lashe zaben shugabancin kasar.
Wallafawa ranar:
Jam’iyyun kawance da ke mara wa gwamnatin sun bayyana ikirarin da shugabannin addinan suka yi da cewa ya yi hannun riga da matsayinsu na iyayen al’umma.
A jiya juma’a Kwamitin Tsaron MDD ya gudanar da zama na musamman dangane da halin da ake ciki a Congo, to sai dai an tashi ba tare da fitar da wata sanarwa ba saboda bambancin ra’ayi a tsakanin manyan kasashen duniya kan halin da ake ciki a kasar.
A gobe lahadi ne ya kamata a fitar da sakamakon zaben shugabancin kasar ta Congo, to sai dai hukumar zabe ta ce abu ne mai yiyuwa a dage ranar, yayin da ‘yan adawa ke cewa ana neman murda sakamakon ne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu