Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

Tshisekedi ya lashe zaben Jamhuriyar Congo

Hukumar zaben Jamhuriyar Congo CENI, ta bayyana Felix Tshisekedi, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da ya gudana a ranar 30 ga watan Disamban da ya gabata.

Zababben shugaban kasar Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo mai jiran gado Félix Tshisekedi.
Zababben shugaban kasar Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo mai jiran gado Félix Tshisekedi. REUTERS/Baz Ratner/File Photo
Talla

Yayin bayyana sakamakon da safiyar yau, hukumar zaben ta ce Felix Tshisekedi ya samu nasarar ce bayan lashe kashi 38 da rabi na kuri’un da aka kada.

A ranar Lahadi ya kamata a bayyana sakamakon zaben, amma hakan bai samu, saboda rashin kammala tattara sakamakon kuri’un da aka kada, a wasu sassan kasar ta Jamhuriyar Congon.

A lokacin da yake bayyana sakamakon zaben da sanyin safiyar yau Alhamis, shugaban hukumar zaben kasar CENI, Corneille Nangaa, ya ce Felix Tshisekedi ya samu kuri’u miliyan 7, yayin da abokin hamayyarsa Martin Fayulu shi ma daga bangaren ‘yan adawa ya samu kuri’u miliyan 6 da dubu 400.

Emmanuel Shadary dan takarar gwamnati shi ne na karshe tsakanin manyan ‘ya takarar neman maye gurbin shugaba Joseph Kabila bayan samun kuri’u miliyan 4 da dubu 400.

Wannan nasara dai ta baiwa Felix Tshisekedi damar kafa tarihin zama dan adawa na farko da ya karbe gwamnati a Jamhuriyar Congo tun bayan samun ‘yancin kan kasar a shekarar 1960 daga Belgium.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.