An yi wa fursunoni 700 afuwa a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo
Sabon shugaban Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo Felix Tshisekedi ya rattaba hannu kan kudurin doka da ke bayar da izinin sakin fursunonin siyasar kasar, daya daga cikin alkawurran da ya dauka cikin jawabin rantsar da shi.
Wallafawa ranar:
Babban jami’in gwamnati a fadar shugaban Vital Kamerhe, shi ne ya bayar da haske dangane da wannan mataki, inda ya ce daga cikin wadanda aka yi wa afuwar har da wasu sanannun ‘yan adawa wato Firmin Yangambi da Franck Diongo.
A jimilce fursunonin siysa 700 ne wannan mataki ya shafa a sassa daban daban na kasar, kuma ana iya sallamar su daga gidajen yari kowane lokaci daga yau alhamis.
Sakin fursunonin siyasa, na daga cikin muhimman bukatun da ‘yan adawa suka gabatar wa tsohon shugaba Joshep Kabila tun shekara ta 2016, kafin daga bisanin Tshisekedi wanda tsohon dan adawa ne ya dauki wannan alkawari lokacin da yake jawabi a ranar da ya karbi ragamar mulkin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu