Isa ga babban shafi
Afrika-Duniya

Yunkurin samar da tallafi don magance matsallar yanayi a Duniya

Shugabannin kasashen duniya, da ke halartar taro kan kare muhalli a Kenya, sun yi alkawarin baiwa kasashen Afrika tallafin dala biliyan 22 da rabi, domin magance barazanar da dumamar yanayi ke yiwa dazuka a nahiyar.

Zaman taron kasashen Duniya-One planet Summit a Kenya
Zaman taron kasashen Duniya-One planet Summit a Kenya Ludovic MARIN / AFP
Talla

Yunkurin samar da tallafin na zuwa ne, bayan da wani rahoto ya nuna cewa, yankin gabashin nahiyar Afrika kadai, ya tafka asarar akalla kadada miliyan 6 na dazuka a wannan karni, yankin da a baya ya kunshi, nau’ikan itatuwa, da dabbobin da babu irinsu a sauran sassan Duniya.

Daya daga cikin ‘yan kungiyar da ke fafutukar kare muhalli, Mustafa Kadi daga jamhuriyar Nijar, yayi kira zuwa Shugabanin kasashe da fatan za su yi aiki da alkawuran da za su dau a zaman taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.