Isa ga babban shafi
Faransa-Yanayi

Kungiyoyi a Faransa sun gurfanar da gwamnati gaban Kotu kan sauyin yanayi

Wasu kungiyoyin fararen hula da suka hada da Greenpeace da Oxfam sun gurfanar da gwamnatin Faransa a kotu inda suke kalubalantar ta kan rashin daukar matakan da suka dace na shawo kan matsalar sauyin yanayi.

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, wanda ke ci gaba daukar matakan ganin kasashen duniya sun mutunta yarjejeniyar yanayi ta birnin Paris da ke da nufin rage sinadaran hayakin da kamfanoni ke fitarwa a sassan duniya.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, wanda ke ci gaba daukar matakan ganin kasashen duniya sun mutunta yarjejeniyar yanayi ta birnin Paris da ke da nufin rage sinadaran hayakin da kamfanoni ke fitarwa a sassan duniya. Ludovic Marin/Pool via REUTERS
Talla

Kungiyoyin masu zaman kan su, sun shigar da karar gwamnatin kan abinda suka kira rashin mutunta ka’idojin takaita gurbatar muhali da kasar ta rattaba hannu a kai.

A cewar Kungiyoyin da suka hada da Greenpeace, Oxfam, da kuma gidauniyar nan da ke mayar da hankali wajen kare muhalli suna kan bakar su don ganin hakar su ta cimma ruwa kan batun wanda suka bayyana da hanya daya tilo da za ta tabbatar da wanzuwar dan adam a ban kasa.

Cikin takaddar karar da suka gabatar gaban kotu, hadakar kungiyoyin sun zargin gwamnatin Faransa da sakaci kan batun da ya shafi yaki da dumamar yanayi.

Tun a jiya Litinin ne dai wasikar da ke tabbatar da shigar da karar ta isa fadar shugaba Emmanuel Macron wadda ta bai wa gwamnatin Faransa wa’adin watanni biyu don amsa kiran kotu.

Laura Monnier jami’ar yada labaran Greenpeace ta ce karar mataki ne na farko da kungiyoyin suka dauka kafin mataki na gaba matukar gwamnatin ta gaza samar da gyara a batun.

A cewarta fatansu shi ne ganin gwamnatin Faransa ta kawo gyara tare da daukar matakan da suka dace don tunkarar kalubalen na dumamar yanayi.

A shekarar 2015, wata kotu a Netherland ta zartas da hukunci kan Faransar inda ta tilasta mata daukar matakan rage gurbatar muhalin da kamfanonin kasar ke fitarwa ta hanyar hayaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.