Isa ga babban shafi
Faransa

Masu zanga-zanga sun sake fita a Faransa sai dai adadi ya ragu

Dubban masu sanye da rigunan dorawa sun sake gudanar da zanga-zanga a sassan Faransa karo na biyar a wannan Asabar, wadda suka saba yi a karshen kowane mako.

Wasu masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Faransa yayin tattaki zuwa Champs-Elysées dake birnin Paris da safiyar ranar Asabar. 15/12/2018.
Wasu masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Faransa yayin tattaki zuwa Champs-Elysées dake birnin Paris da safiyar ranar Asabar. 15/12/2018. RFI
Talla

Ma’aikatar cikin gidan kasar ta ce an samu raguwar mutanen da suka fita zanga-zangar ta ranar Asabar sosai, la’akari da cewa kimanin mutane dubu 66,000 ne suka fita wanda adadin shi ne rabin wadanda suka fita a makon da ya gabata da yawansu ya kai akalla dubu 125.

A birnin Paris masu zanga-zangar adawa da gwamnati dubu 2,200 ne kawai suka fita yayinda aka girke ‘yan sanda dubu 8000. Zalika yawan wadanda aka kama ya tsaya ne kan 168, kasa da sosai da akalla masu zanga-zanga 1000 da aka tsare a makon da ya gabata, saboda tayar da tarzoma.

Sai dai wata kuri’ar jin ra’ayi da jaridar Le Journal Du Dimanche dake kasar ta gudanar, ta nuna cewa farin jinin shugaba Macron ya ragu zuwa kashi 23 daga kashi 62 da yake da shi tsakanin Faransawa.

Gwamnatin Macron ta soma fuskantar gagarumin kalubalen ne, bayan zartas da karin farashin albarkatun mai da wasu sauye-sauyen da ta bayyana a matsayin shirin karfafa tattalin arzikin kasar, lamarin da ya haddasa zanga-zanga a sassan kasar da ta juye zuwa tarzoma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.