Isa ga babban shafi
Faransa

Masu zanga-zanga sun yiwa 'yan sanda rotse a Paris

Jami'an 'yan sanda a Faransa sun kama mutane 39, biyo bayan arrangamar da suka yi da masu zanga-zangar adawa da karin farashin albarkatun mai a safiyar wannan Asabar. 

Jami'an 'yan sandan Faransa, yayin arrangama da masu zanga-zangar adawa da karin farashin albarkutun mai, a birnin Paris. 24/11/2018.
Jami'an 'yan sandan Faransa, yayin arrangama da masu zanga-zangar adawa da karin farashin albarkutun mai, a birnin Paris. 24/11/2018. REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Zanga-zangar ta juye zuwa tashin hankali ne bayan wasu daga cikin daruruwan mutanen da suka yi fitar dango, suka soma jifan jami'an tsaro da duwatsu hadi da sauran abubuwa masu hadari, a yankunan dake gaf da Champs-Elysees a birnin Paris.

Ministan cikin gidan Faransa Christophe Castaner, ya ce akalla masu zanga-zangar 1,500 ne suka tunkari jami'an tsaron kasar domin arrangama, bayan barkewar tarzomar.

tashin hankalin ya zo ne bayanda gwamnatin Faransa ta kara yawan jami’an ‘yan sanda a birnin Paris, domin zama cikin shirin ko ta kwana, yayinda dubban jama’a ke sake gudanar da zanga-zangar adawa da karin farashin albarkatun man fetur a karo na uku.

Zuwa yanzu dai dubban masu zanga-zangar sanye da riguna kalar dorawa, sun tsare hanyoyi da dama a sassan Faransa.

Hukumomin tsaron kasar ta Faransa sun ce an kara yawan jam’an ‘yan sandan da aka girke a Paris daga dubu uku zuwa dubu biyar, zalia za’a kara aikewa da Karin jami’an dubu biyar, zuwa sassan kasar domin sa ido kan dubban masu zanga-zangar masu sanye da riguna ruwan dorawa.

Zanga-zangar da ta juye zuwa tashin hankali, na a matsayin kalubale mafi girma da gwamnatin shugaban Faransa Emmanuel Macron ke fuskanta, bayan shafe watanni 18 da darewa shugabancin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.