Isa ga babban shafi
Faransa

Masu bincike a Faransa sun gano mutumen da ya taimakawa Cherrif a Strasbourg

Jami’an yaki da ta’addanci a Faransa sun ce nan gaba kadan zasu gurfanar da mutumin da ake zargin alaka da dan bindigar da ya kai hari kasuwar kirsimeti dake Strasbourg, inda ya kashe mutane 5 yanzu haka da kuma jikkata wasu a harin garin Strasbourg.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron a lokacin da ya ziyarci kasuwar kirismeti a garin Strasbourg
Shugaban Faransa Emmanuel Macron a lokacin da ya ziyarci kasuwar kirismeti a garin Strasbourg Jean-Francois Badias/Pool via REUTERS
Talla

Majiyar shari’ar kasar tace ana tuhumar mutumin da taimakawa Cherif Chekatt da bindigar da ya kai harin, wanda babban laifi ne a Faransa.

Yanzu haka an saki mutane 6 da aka tsare bayan harin, cikin su harda iyayen Cherif.

Faransawa da dama ne suka nuna damuwa tareda bukatar hukumomin kasar sun karfafa matakan tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.