Isa ga babban shafi
Burkina Faso

'Yan bindiga sun jefa Burkina Faso cikin zaman makoki

Al’ummar  Burkina Faso na zaman makoki sakamakon wani kazamin hari da wasu ‘yan bindiga suka kai wa cocin Katolika da ke yankin Dablo a arewacin kasar, inda nan take suka kashe mutane 6 ciki har da limamin cocin.

Jami'an tsaron Burkina Faso na cikin shirin ko-ta-kwana
Jami'an tsaron Burkina Faso na cikin shirin ko-ta-kwana African Stand
Talla

Harin na zuwa ne kwanaki biyu bayan da jam'ian tsaro na musamman daga Faransa suka kai samame kasar, inda suka kubutar da ‘yan kasashen waje da ‘yan bindigan suka yi garkuwa da su.

Wasu shaidu sun ce, maharan da yawansu ya kai kimanin 30, sun dirar wa cocin ne a daidai lokacin da masu ibada ke cikin addu'a.

Maharan sun kuma kona cocin da wasu shaguna kafin daga bisani su doshi wata cibiyar kula da marasa lafiya, inda suka sace kayayyki da kuna kona motar shugabar kula da cibiyar.

Jama'ar yankin na cikin dari-dari, sannan kuma hada-hadar kasuwanci da zirga-zirga ta dakata kamar yadda Ousmane Zongo, daya daga cikin mazauna yankin ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.