Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Harin ta'addanci a Majami'ar Burkina Faso ya hallaka mutane 6

Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan jihadi ne sun hallaka akalla mutane 6 ciki har da limamin Majami'a yayin wani farmaki da suka kai kansu lokacin da su ke tsaka da Ibada a garin Silgadji da ke arewacin kasar Burkina Faso.

Dakarun sojin Burkina Faso lokacin da su ke kokarin farmakar maboyar 'yan ta'adda a wani yanki na kasar
Dakarun sojin Burkina Faso lokacin da su ke kokarin farmakar maboyar 'yan ta'adda a wani yanki na kasar ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Wata majiyar tsaro a garin na Silgadji da ke gab da Djibo ta bayyanawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, harin ya faru ne da tsakar rana lokacin da jama'a ke kokarin barin majami'ar bayan kammala ibadar mako-mako.

Rahotanni sun ce maharan wadanda suka je harabar majami'ar akan babura sun bude wuta akan jama'a lamarin da ya razana mutane inda nan take aka tarwatse, yayinda rahotanni ke cewa kawo yanzu akwai mutane 2 da suka bace ba a san inda suka fada ba, bayan afkuwar harin.

Wannan dai ne karon farko da Burkina Faso ke fuskantar hari kan majami'a, yayinda a baya yafi shafar jami'an tsaro ko kuma sashen mabiya addinin Islama, ciki har da wanda ya kashe wani fitaccen limamin mabiya musulunci.

Tun farko fara hare-haren ta'addanci a Burkina Faso galibi ya fi tsananta a yankin arewacin kasar kafin daga bisani ya fantsamu zuwa sassan kasar ciki har da Ouagadougou babban birnin Kasar.

Kungiyoyin ta'addanci da suka kunshi Ansarul Islama da GSIM mai ikirarin taimakon Musulmi da kuma IS ne suka addabi tsaron kasar ta Burkina Faso, wanda ya kai kasar ga shiga rundunar yaki da ta'addanci a yankin Sahel.

Ko cikin watan Fabarairu, wani harin ta'addanci a birnin Nohao da ke tsakiyar kasar ya yi sanadin mutuwar wani Limamin Majami'ar Spain Father Cesar Farnandez.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.