Rikici ya hallaka mutane 46 a Burkina Faso
Rahotanni daga Burkina Faso na cewa akalla mutane 46 ne suka mutu cikin makon nan sakamakon hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi da kuma rikicin kabilanci a sassan tsakiyar kasar.
Wallafawa ranar:
Tun farko dai mahukuntan kasar sun sanar da mutuwar mutane 13 sakamakon rikicin da ya barke a kauyen Yirgou na yankin Barsalogo a ranakun Talata da Laraba, sai dai kakakin gwamnatin kasar ya ce adadin wadanda suka mutun ya karu zuwa 46 a yau Juma’a.
A cewar kakakin gwamnatin Remis Fulgance rikicin ya faro ne daga wani harin ‘yan bindiga da ya hallaka mutane 7 cikin har da shugaban kauyen.
Sai dai kuma barkewar sabon rikici bayan harin a cewarsa ya haddasa asarar tarin rayuka wanda a yau ya kai 46.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu