Isa ga babban shafi
Sudan

An tsamo gawarwakin mutane 40 daga kogin Nilu a Sudan

Masu fafutukar kare hakkin dan adam da ‘yan adawa a Sudan, sun ce an tsamo gawarwakin mutane akalla 40 daga kogin Nilu da ke babban birnin kasar Khartoum.

Kogin Nilu da ya ratsa  Khartoum, babban birnin kasar Sudan.
Kogin Nilu da ya ratsa Khartoum, babban birnin kasar Sudan. AFP/Ebrahim Hamid
Talla

Wannan al’amari dai ya zo ne bayan da a ranar litinin, sojojin na Sudan suka yi amfani da karfi wajen tarwatsa dubban masu zanga-zanga a Khartoum, inda suka bude musu wuta, matakin da yayi sanadin hallakawa da kuma jikkata mutane da dama.

Kungiyar likitocin Sudan ta ce gawarwakin mutanen na daga cikin adadin fararen hula 100, da sojojin kasar suka hallaka, a lokacin da suka yi amfani da karfi wajen tarwatsa sansanin masu zanga-zangar neman mikawa farar hula mulki a ranar Litinin.

Ranar Talata 4 ga watan Yuni, Sojoji da ke kan karagar mulkin kasar Sudan suka soke yarjejeniyar raba madafun iko da kuma kafa gwamnatin hadin gwiwa da fararen hula, wadda a baya suka cimma matsaya akai, tsakaninsu da shugabannin masu zanga-zanga.

Matakin na kunshe ne, a jawabin da shugaban majalisar mulkin sojin kasar ya gabatar a daren ranar litinin, bayan da sojojin suka yi amfani da karfi don kawo karshen tarzomar da ake yi a kasar.

Shugaban majalisar mulkin sojin na Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya ce bayan soke yarjejeniyar da aka kulla tsakanin bangarorin biyu, za gudanar da zabukan kafa sabuwar gwamnatin farar hula a cikin watanni 9 masu zuwa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.