Kungiyar 'yan uwa musulmi ta zargi gwamnatin Masar da kashe Morsi
Kungiyar 'yan uwa Musulmi a Masar ta zargi gwamnatin Masar da kashe tsohon shugaban kasa Mohammed Morsi a tsanake.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kungiyar ta ce da gangan gwamnati ta tsare shugaban cikin daki ba tare da barin wani ya kai gare shi ba da hana shi magunguna da kuma bashi abinci mara inganci.
Shi ma shugaban Turkiya Recep Tayip Erdogan ya zargi shugaban kama karya na Masar da kashe tsohon shugabana kasar, inda ya ce tarihi ba zai taba mantawa da wadanda suka daure shi ba, kuma suka yi barazanar kashe shi ba.
Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad al-Thani ya bayyana kaduwar sa da mutuwar Morsi, inda ya aike da sakon ta’aziya ga iyalan sa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu