Isa ga babban shafi
Madagascar-Duniya

Duniya na shakku kan maganin corona saboda Afrika ce ta samar da shi - Madagascar

Shugaban Madagascar Andry Rajoelina yace magani da kuma rigakafin annobar coronavirus na ‘Covid-Organics’ da kwararru kan lafiya a kasar suka samar, na warkar da cutar ta coronavirus cikin kwanaki 7 zuwa 10.

Shugaban kasar Madagascar Andry Rajoelina a Antananarivo, babban birnin kasar, yayin kaddamar da ‘Covid-Organics’, magani kuma rigakafin cutar coronavirus na gargajiya.
Shugaban kasar Madagascar Andry Rajoelina a Antananarivo, babban birnin kasar, yayin kaddamar da ‘Covid-Organics’, magani kuma rigakafin cutar coronavirus na gargajiya. © AFP / Rijasolo
Talla

Bayanan Shugaba Rajoelina na zuwa ne a daidai lokacin da ya rasa goyon bayan hukumar lafiya ta duniya WHO, wadda ta nuna shakku kan ingancin maganin an ‘Covid-Organics’, wanda tuni kasashen Afrika da dama ciki har da Najeriya, Nijar da kuma Tanzania da Guinea Bissau suka karbi maganin don amfani da shi.

Yayin zantawa da kafafen yada labaran RFI da France24, shugaba Rajoelina yace maganin da aka samar a kasarsa ta Madagascar na fuskantar adawa da kushe ne saboda ya fito ne daga nahiyar Afrika ba daya daga cikin kasashen Turai ba.

01:13

Shugaban Madagascar Andry Rajoelina kan ingancin maganin Covid-Organics mai warkar da cutar corona

Salissou Hamissou

Alkalumman hukumomin lafiya a baya bayan nan sun nuna cewar Madagascar da ta samar da maganin cutar coronavirus na ‘Covid-Organics’ har yanzu na da jumillar mutane 186 ne da suka kamu da coronavirus, yayinda 105 suka warke, babu kuma wanda ya rasa ransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.