Isa ga babban shafi
Burkina Faso - Juyin mulki

An fara samun bayanai kan halin da tsohon shugaba Kabore ke ciki

Hambararren shugaban Burkina Faso, Roch Marc Christian Kabore, yana cikin koshin lafiya kuma sojoji suna tsare a wani gida da ke fadar shugabancin kasar, kamar yadda wata majiya ta jam'iyyarsa ta bayyana a ranar Laraba.

Shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré.
Shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré. AP - Michel Euler
Talla

Halin da Kabore da kuma inda yake ya zama muhimmin batu tun bayan da wasu sojoji suka hambarar da shi daga mulki a ranar Litinin, inda Majalisar Dinkin Duniya ke jagorantar kiran da a sake shi.

A baya bayan nan ne kuma, wata majiya a jam’iyyar  tsohon shugaba Kabore ta People's Movement for Progress MPP, yana cikin koshin lafiya, amma babu karin bayan ikan ko yana cikin halin kunci ko akasin haka.

Majiyar ta kara da cewar, Kabore na karkashin dauri ne na talala, ba a sansanin soji. ba, zalika yana da likita, kuma yana da damar yin amfani da wayar salula, amma a cikin matakan sa ido.

Shugaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore, a birnin Ouagadougou yayin kada kuri'a a zaben shugabancin kasar na shekarar 2020.
Shugaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore, a birnin Ouagadougou yayin kada kuri'a a zaben shugabancin kasar na shekarar 2020. Issouf SANOGO AFP

A shekarar 2015 aka zabi Kabore mai shekaru 64, bayan boren da ya tilastawa Blaise Compaore barin mulki, wanda ya hau kan karagar mulki tun shekara ta 1987.

An sake zaben tsohon shugaba Kabore a shekara ta 2020, amma a 2021 ya fuskanci fushin ‘yan kasar, sakamakon karuwar hare-haren 'yan ta’adda masu ikirarin Jihadi da karfin tsiya.

A ranar Litinin, Jami’an sojin Burkina Faso suka kama shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore, wanda ya sha fuskantar zanga-zangar adawa daga dubban jama’a akan gazawarsa wajen dakile hare-haren ‘yan ta’adda a kasar.

A halin yanzu dai kasar da ke yankin Sahel tana karkashin kungiyar sojoji ‘yan Kishin Kasa ta MPSR, wadda  Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba ke jagoranta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.