Isa ga babban shafi
Faransa-Algeria

Faransa za ta biya diyyar wadanda suka taya ta yaki a Algeria shekaru 60 baya

Shekaru 60 bayan kawo karshen yakin neman ’yancin kan Algeria da aka gwabza, majalisar dokokin Faransa ta amince da wani kudiri da zai nemi gafarar ‘yan kasar da suka yi wa Faransa yaki, abinda zai bada damar biyan wasu iyalansu diyya.

Shugaba Emmanuel Macron yayin jawabinsa gaban zaman majalisar Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron yayin jawabinsa gaban zaman majalisar Faransa. Bertrand Guay Pool/AFP
Talla

Wannan daftari ya biyo bayan matsayin shugaba Emmanuel Macron wanda a ranar 20 ga watan Satumba bara ya nemi gafarar Yan kasar Algeria da suka taimakawa sojojin Faransa yaki da masu fafutukar neman yancin kan kasar su amma akayi watsi  da su bayan kasar ta sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya a ranar 18 ga watan Maris na shekarar 1962.

Shekaru 60 bayan haka, raunin da yakin da ya lakume rayukan mutane kusan dubu 500 ya haifar bai warke ba, abinda ya haifar da mahawara a majalisun Faransa guda biyu dangane da makomar wadannan sojoji.

Yan majalisun dokoki da na datatwan kasar, akasarin su daga bangaren masu ra’ayin rikau sun amince da daftari na hadin gwuiwa a makon jiya dangane da bukatar sauya matsayin kasar akan lamarin.

Sanata marie-Pierre yace sun kama hanyar sasantawa dangane da abinda ya faru a baya, yayin da Laurent Burgoa yace babu wani lafazi da zai kauda radadin abinda ya faru.

Kudirin dokar ya bada shawarar biyan diyyar tsakanin euro 2,000 zuwa 15,000 ga iyalan sojojin kusan 50,000 akan kudi euro miliyan 310 a cikin shekaru 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.