Isa ga babban shafi
Isra'ila-Daular Larabawa

Masar na karbar bakoncin ganawar Isra'ila da Daular Larabawa

Kasar Masar na karbar bakoncin ganawar shugabannin Isra'ila da na Hadaddiyar Daular Larabawa don yin wasu shawarwarin da ba a taba gani ba, daidai lokacin da yakin Ukraine ke ruguza kasuwannin makamashi da abinci da kuma manyan kasashen duniya wajen cimma yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Shugaba Abdel Fattah Al-Sissi tare da Firaministan Isra'ila Naftali Bennett da kuma Yarima mai jiran gado na hadaddiyar daular larabawa Sheikh Mohamed ben Zayed.
Shugaba Abdel Fattah Al-Sissi tare da Firaministan Isra'ila Naftali Bennett da kuma Yarima mai jiran gado na hadaddiyar daular larabawa Sheikh Mohamed ben Zayed. VIA REUTERS - HANDOUT
Talla

Hakan dai na zuwa ne kusan wata guda bayan da Rasha ta mamaye kasar Ukraine a wani mataki da ya haifar da fargaba game da tsaro da kuma tashin farashin man fetur da alkama da sauran muhimman kayayyaki.

Masar, Isra'ila da Hadaddiyar Daular Larabawa kawayen Amurka ne amma kawo yanzu sun kaucewa daukar matsaya kan Rasha game da yakin da ta ke yi da Ukraine.

Sanarwar da ofishin firaministan Isra’ila Naftali Bennett ta fitar ta ce, sakamakon abubuwan da suka faru a duniya, shugabannin sun tattauna kan dangantakar dake tsakanin kasashen uku da kuma hanyoyin karfafa su a dukkan matakai.

A ganawar da suka yi, shugabannin uku sun tattauna kan batun makamashi, harkokin kasuwanci da kuma yadda za a inganta hanyoyin samar da abinci.

Kafofin yada labaran Isra'ila sun ce shugabannin za su kuma tattauna kan rahotannin da ke cewa Iran da manyan kasashen yammacin duniya ciki har da Amurka na daf da farfado da yarjejeniyar nukiliyar 2015.

Isra’ila dai na adawa da yarjejeniyar da aka kulla domin hana babbar makiyiyarta wato Iran mallakar makamin nukiliya, burin da kasar ta ke musantawa a ko da yaushe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.