Isa ga babban shafi
FARANSA-DAULAR LARABAWA

Daular Larabawa zata sayi jiragen yaki 80 daga Faransa

Kasar Daular Larabawa ta rattaba hannu akan kwangilar sayen jiragen yakin Faransa kirar Rafael Jet guda 80 akan kudi euro biliyan 14 lokacin ziyarar da shugaba Emmanuel Macron ya kai kasar.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Yariman Abu Dhabi Mohammed bin Zayed al-Nahyan
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Yariman Abu Dhabi Mohammed bin Zayed al-Nahyan Thomas SAMSON AFP
Talla

Wannan kwangilar wadda itace irin ta mafi girma a tarihin cinikin jiragen yakin Rafael Jet da Faransa ke kerawa, ya biyo bayan tattaunawar da Yariman Abu Dhabi, Sheikh Mohammed bin Zayed yayi da shugaba Emmanuel Macron dake ziyarar kasar.

Daular Larabawa wadda ke zama daya daga cikin manyan abokan kasuwancin Faransa ta kuma bada odar kera mata jiragen ruwan dake daukar jiragen saman yaki masu saukar ungula guda 12 akan kudin da ya kai euro biliyan 17.

Shugaba Emmanuel Macron da Yariman Abu Dabi, Mohamed bin Zayed tare da ministocin su bayan rattaba hannu a yarjejeniyar kasuwanci
Shugaba Emmanuel Macron da Yariman Abu Dabi, Mohamed bin Zayed tare da ministocin su bayan rattaba hannu a yarjejeniyar kasuwanci Thomas Samson AFP

Fadar shugaban Faransa ta bayyana wadannan kwangiloli a matsayin masu muhimmanci ga kasashen biyu da kuma tabbatar da aniyar su ta aiki tare domin inganta tsaron su.

Gidauniyar Mubadala dake Abu Dhabi ita ma tayi alkawarin zuba jarin euro biliyan 8 a harkokin kasuwancin kasar Faransa, yayin da aka tsawaita lasisin reshen Abu Dhabi dake wurin aje kayan tarihin Louvre na shekaru 10, wanda zai kai zuwa shekarar 2047.

Sanfurin jiragen Rafael Jet da Faransa ke kerawa
Sanfurin jiragen Rafael Jet da Faransa ke kerawa AP

Rahotan majalisar dokokin Faransa yace Daular Larabawa ce ta biyar cikin manyan ‘Yan kasuwan masana’antar kayan yakin Faransa na kudin da ya kai euro biliyan 4 da miliyan 700 daga shekarar 2011 zuwa shekarar 2020.

Ana saran shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ziyarci kasashen Qatar da Saudi Arabiya a ziyarar kwanaki biyu da ya fara, wadda zata bashi damar kulla irin wadannan yarjeniyoyi da dama.

Macron na samun rakiyar tawagar manyan Yan kasuwar Faransa a wannan tafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.