Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Masu adawa da juna a Sudan ta Kudu sun amince da kafa sojin hadaka

Shugabannin Sudan ta Kudu da ke rikici da juna sun cimma yarjejeniya game da kafa sojin-hadaka, biyo bayan jan-kafar da aka yi ta samu dangane da kawo karshen takun-sakarsu.

Mataimakin shugaban Sudan ta Kudu Riek Machar (hagu) da shugaba Salva Kiir (dama)
Mataimakin shugaban Sudan ta Kudu Riek Machar (hagu) da shugaba Salva Kiir (dama) ALEX MCBRIDE / AFP
Talla

Shugaba Salva Kiir da babban dan adawarsa kuma mataimakinsa, Riek Machar sun amince da kafa rundunar sojin hadin guiwa, batun da ke cikin gaggan batutuwan da bangarorin biyu suka gaza fahimtar juna a kai, lamarin da ya haifar da cikas game da aiwatar da yarjejeniyarsu ta shekarar 2018 wadda aka yi fatan za ta kawo karshen zubar da jinin tsawon shekaru biyar da aka yi ana yakin basasa a kasar.

Martin Abucha, shi ne wakilin Machar da ya rattaba hannu kan yarjejejeniyar, ya kuma ya ce, zaman lafiya ya ta’allaka ne da tsaro, sannan sun cimma gaci a cewarsa.

Ministan Kula da Harkokin shugaban kasar ta Sudan ta Kudu , Barnaba Marial Benjamin ya yaba da wannan yarjejeniya wadda aka cimma bayan makwabciyarsu Sudan ta shiga tsakani don samar da masalaha.

A ‘yan kwanakin nan, an ga yadda bangarorin biyu suka yi tayar da jijiyoyin wuya, al’amarin da ya jefa fargaba a zukatan kasashen duniya kan yiwuwar sake kazancewar tashin hankali a kasar ta Sudan ta Kudu.

Shugabannin biyu, wato Kiir da Machar duk sun samu halartar bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar a birnin Juba a jiya Lahadi, inda suka amince cewa, bangaren Kiir zai samu kashi 60 na sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a kasar, yayin da bangaren Machar ke da kashi 40.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.