Isa ga babban shafi

Rundunar G5 Sahel dake yaki da 'Yan ta'adda ta mutu - Bazoum

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed yace kungiyar G5 Sahel dake yaki da ‘Yan ta’addan da suka addabi wasu kasashen dake ‘Yankin Afirka ta Yamma ta mutu, sakamakon ficewar Mali daga cikin ta.

Shugaba Bazoum Mohammed na Jamhuriyar Nijar
Shugaba Bazoum Mohammed na Jamhuriyar Nijar © RFI
Talla

Yayin wata hira da jaridar kasar Faransa shugaban ya bayyana dalilan da suka saka ficewar Mali daga kungiyar da suka hada da kin bata damar jagorancin karba karba da akeyi a tsakanin kasashen dake cikin tafiyar.

Shugaban kasar Chadi Janar Mahamat Idris Deby tare da shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed
Shugaban kasar Chadi Janar Mahamat Idris Deby tare da shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed © Niger Presidency

Bazoum yace kasar Mali na ci gaba da zama saniyar ware tun bayan juyin mulki na 2 da akayi a kasar a watan Mayun bara, inda kungiyar ECOWAS da ta kasashen Afirka na AU da Majalisar Dinkin Duniya suka sanya mata takunkumin karya tattalin arziki.

Shugaban yace wannan matsala ta Mali na zagon kasa akan hadin kan da kasashen ‘Yankin ke yi wajen tinkarar matsalar tsaro musamman abinda ya shafi ayyukan ta’addanci da masu ikrarin jihadi.

Kasar Mali ta danganta matakin hana ta shugabancin kungiyar da rawar da tace wata kasa ke takawa daga wajen yankin domin kawar da ita, yayin da wasu ke danganta matsayin na ta da kasar Faransa wadda tuni ta fara janye sojojin ta daga kasar saboda juyin mulkin da soji suka yi.

Sojojin Faransa lokacin da suke ficewa daga Gao a kasar Mali
Sojojin Faransa lokacin da suke ficewa daga Gao a kasar Mali AP

Jakadan Faransa a Majalisar Dinkin Duniya Nicolas de Riviere tare da wakilan kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana matukar damuwa dangane da ficewar Mali daga kungiyar hadin kan ta G5 Sahel.

De Riviere yace kasashe 5 dake hadin kai a yankin Afirka ta Yamma suka kafa rundunar G5 Sahel domin shawo kan matsalar da ta addabe su, saboda haka yanzu nauyi na kan su wajen yanke hukunci akan makomar ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.