Isa ga babban shafi

Taron AU zai karkata kan matsalolin ta’addanci da juyin mulki a Afirka

Matsalar ayyukan ta’addanci dake karuwa a kasashen Afirka tare da juyin mulkin da sojoji ke yi wajen kawar da zababbun shugabanni na daga cikin manyan batutuwan da shugabannin kasashen Afirka zasu mayar da hankali akai wajen taron sun a musamman da ke gudana a Equatorial Guinea a wannan juma’a mai zuwa.

Shugaban Hukumar Gudanarwar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat.
Shugaban Hukumar Gudanarwar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat. REUTERS - TIKSA NEGERI
Talla

Shugaban gudanarwar kungiyar Moussa Faki Mahamat Tashe tashen hankulan dake nasaba da ayyukan ta’addanci sun karu daga Libya zuwa Mozambique da kuma daga Mali zuwa Somali, yayin da matsalar ke neman zama ruwan dare a Yankin Sahel da Tafkin Chadi da kuma Gabashin Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo.

Dangane da juyin mulkin soji kuwa da aka gani na baya bayan nan a kasashen Mali da Guinea da Burkina Faso da kuma Sudan, shugaban gudanarwar kungiyar yace matsalar ta taimaka wajen mayar da hannu agogo baya dangane da shirin dimokiradiya.

Sojoji na jan kafa wajen shirya zabe - Mahamat

Mahamat ya kuma bayyana damuwa da tsaikon da ake samu a tsakanin wadannan kasashe wajen gabatar da shirin gudanar da zabe da zummar dawo da shugabannin fararen hula.

Kungiyar kasashen Afirka ta AU da ECOWAS da kungiyar kasashen Turai da Amurka da kuma Majalisar Dinkin Duniya duk sun bayyana damuwa da jinkirin mayar da mulkin fararen hular a wadannan kasashe, yayin da wasu daga cikin su suka sanya takunkumin karya tattalin arziki akan sojojin da suka kifar da gwamnatin.

Ana saran taron ya kuma tattauna matsayin Chadi wadda ke da shugaban soji Mahamat Idris Deby, wanda ya maye gurbin mahaifin sa da kuma Nazari akan alkawarin da yayi na gudanar da zabe bayan watanni 18.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.