Isa ga babban shafi

An fara taron kolin kungiyar Tarayyar Afirka a Malabo

Shugabannin kasashen Afirka na shirin fara gudanar da wani taro na musamman a Malabo a karkashin kungiyar AU wanda zai mayar da hankali akan ayyukan jinkai da yaki da ta’addanci da kuma dakile juyin mulkin da sojoji ke yi a wasu kasashen dake yankin.

Shugaban gudanarwar kungiyar kasashen Afirka AU, Moussa Faki Mahamat.
Shugaban gudanarwar kungiyar kasashen Afirka AU, Moussa Faki Mahamat. © Dursun Aydemir/Anadolu Agency via Getty Images
Talla

Equatorial Guinea ta ce tana sa ran halartar akalla shugabanin kasashen Afirka 20 da kuma wadanda zasu wakilci kasashen su a daidai lokacin da ake bayyana cewar akalla mutane miliyan 113 ke bukatar agajin gaggawa a wannan shekarar daga nahiyar, yayin da ayyukan ta’addanci ke samun gindin zama tare da juyin mulki guda 4 da aka gani a cikin shekaru biyu.

Shugaban gudanarwar kungiyar Moussa Faki Mahamat ya gabatar da jawabin bude taron ga majalisar zartarwar kungiyar inda ya bayyana cewar daga cikin mutane miliyan 113 da ke bukatar taimakon jinkai, miliyan 15 na bukatar sa cikin gaggawa, abinda ya sa za’a kaddamar da gidauniyar taimakawa wadanan mutane a wajen taron a ranar juma’a mai zuwa.

Mahamat ya ce akalla mutane miliyan 30 aka tilastawa barin matsugunan su sakamakon tashe tashen hankula, kuma sama da miliayn 10 daga cikin su yara ne kanana wadanda ke kasa da shekaru 15.

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce daga cikin mutane kusan biliyan guda da rabi dake Afirka, kusan miliyan 282 na fama da matsalar tamowa, adadin da ya karu daga miliyan 49 da ake da shi a shekarar 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.