Isa ga babban shafi

Dakarun MNJTF sun kashe 'Yan ta'adda sama da 30 a tafkin Chdi

Dakarun kawancen kasashen yankin tafkin Chadi mai fama da rikici sun sanar da kashe mayaka masu ikirarin jihadi fiye da 30 a wasu samame biyu da suka kaddamar domin kakkabesu.

Sojojin hadakar da ke karkashin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF daga Najeriya da Nijar da kuma Kamaru sun samu nasarar kashe mayakan ISWAP fiye da 100.
Sojojin hadakar da ke karkashin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF daga Najeriya da Nijar da kuma Kamaru sun samu nasarar kashe mayakan ISWAP fiye da 100. © MNJTF
Talla

Rundunar hadin gwiwa ta (MNJTF) ta ce hare-haren kasa da na sama da suka kai a yankin Tumbun Rago da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya sun yi nasarar kashe 'yan ta'adda fiye da 25.

Cikin wata sanarwa MNJTF tace, wani harin na daban da ta kai Kirta dake Wulgo duk ta bangaren jihar ta Barno ya yi sanadin mutuwar ‘yan ta’adda biyar.

Sanarwar ta wannan litinin tace wasu sojojin Chadi da na Nijar 7 sun dan samu raunuka.

Rundunar ta kaddamar da hare-haren ne a makon da ya gabata a karkashin wani farmaki mai taken ‘Operation Lake Integrity’.

Yankin kudu maso yammacin tafkin Chadi ya zama mafakar mayakan Boko Haram da kuma kishiyarta ta IS da ke yammacin Afirka (ISWAP), wadanda ke buya a tsibirai da ke cikin tudu mai fadin gaske.

A shekarar 2015, kasashe hudu da ke makwabtaka da tafkin -- Chadi, Kamaru, Nijar da Najeriya – tare da kasar Benin suka sake farfado da kungiyar ta MNJTF, wadda aka kafa a shekarar 1994 amma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.